Pular para o conteúdo
Publicidade

As 10 parábolas mais importantes de Jesus

Por Bíblia Online  - 

Jesus ensinou lições profundas por meio de parábolas, histórias curtas e simbólicas que comunicam verdades espirituais. Cada parábola tem um significado especial e atemporal, revelando o caráter de Deus e ensinando como viver como cristãos. Aqui estão 10 das parábolas mais marcantes e suas lições:

1. Parábola do Semeador (Mateus 13:3-9)

Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, "Wani manomi ya fita don shuka irinsa. Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka. Duk mai kunnen ji, ji."

A parábola do semeador fala sobre a receptividade das pessoas à Palavra de Deus. Cada tipo de solo representa diferentes maneiras de receber e aplicar o Evangelho em nossas vidas. Somente um coração fértil e comprometido pode dar frutos espirituais abundantes.

2. O Bom Samaritano (Lucas 10:25-37)

Misalin mutumin Samariya nagari

Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, "Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?"

Yesu ya amsa ya ce, "Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?"

Sai ya amsa ya ce, " Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka; kuma, Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ "

Yesu ya ce, "Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu."

Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, "Shin, wane ne maƙwabcina?"

Yesu ya amsa ya ce, "Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.

"A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?"

Masanin dokoki ya amsa ya ce, "Wanda ya nuna masa jinƙai."

Yesu ya ce masa, "Je ka, ka yi haka nan."

Essa parábola nos ensina sobre o amor ao próximo, independentemente de raça ou religião. O samaritano ajudou um desconhecido, mostrando que a verdadeira fé se revela no amor ao próximo.

3. A Ovelha Perdida (Lucas 15:4-7)

"In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata. Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.

Deus é como o pastor que busca incessantemente uma ovelha perdida. Essa parábola revela o amor incansável de Deus pelos pecadores, celebrando a alegria no céu quando alguém se arrepende.

4. O Filho Pródigo (Lucas 15:11-32)

Misalin ɗa da ya ɓace

Yesu ya ci gaba da cewa, "Akwai wani mutum wanda yake da ya’ya biyu maza. Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, Baba, ba ni rabon gādona.Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.

"Bayan yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu. Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.

"Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, "Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka."  Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

"Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

"Sai ɗan ya ce masa, Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.

"Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.Sai suka fara shagali.

"Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. Bawan ya ce, Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.

"Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!

"Sai mahaifin ya ce masa, Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ "

A parábola do filho pródigo fala sobre o perdão e o amor incondicional de Deus por Seus filhos, mesmo quando se desviam.

5. A Pérola de Grande Valor (Mateus 13:45-46)

"Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’uluai masu kyau. Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

Jesus ensina que o Reino de Deus é o bem mais precioso e devemos estar dispostos a renunciar tudo para possuí-lo.

6. O Fariseu e o Publicano (Lucas 18:9-14)

Misalin Bafarisiye da mai karɓar haraji

Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, "Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.

"Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.

"Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi."

Essa parábola nos lembra que Deus valoriza um coração humilde e arrependido, em contraste com a arrogância espiritual. O publicano, ao reconhecer seus pecados, foi justificado diante de Deus.

7. Os Talentos (Mateus 25:14-30)

Misalin talenti

"Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar. Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu. Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.

"Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.

"Maigidansa ya amsa ya ce, Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!

"Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.

"Maigidansa ya amsa ya ce, Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!

"Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.

"Maigidansa ya amsa ya ce, Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.

" Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma. Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

Nesta história, Jesus ensina sobre a responsabilidade de usar bem os dons e recursos que Deus nos confiou. A fidelidade nas pequenas coisas abre portas para bênçãos maiores.

8. O Rico e Lázaro (Lucas 16:19-31)

Mai arziki da Lazarus

"An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.

"Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. Sai ya yi masa kira ya ce, Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.

"Amma Ibrahim ya ce, Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.

"Ya amsa ya ce, To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, gama ina da yan’uwana biyar maza. Bari ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.

"Ibrahim ya amsa ya ce, Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.

"Sai ya ce, A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.

"Amma ya ce masa, In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ "

A parábola alerta sobre as consequências de negligenciar os necessitados e viver para si mesmo. Também destaca a realidade do julgamento e da vida após a morte.

9. O Joio e o Trigo (Mateus 13:24-30)

Misalin ciyayi

Yesu ya ba su wani misali. "Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa. Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa. Sa’ad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.

"Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, Ranka daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?

"Sai ya ce, Abokin gāba ne ya yi wannan.

"Bayin suka tambaye shi suka ce, Kana so mu je mu tuttumɓuke su?

"Ya amsa ya ce, A’a, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar. Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ "

Essa história simboliza o bem e o mal coexistindo no mundo até o julgamento final, quando Deus fará a separação entre os justos e os ímpios.

10. As Dez Virgens (Mateus 25:1-13)

Misalin budurwai goma

"A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.

"Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!

"Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.

"Su kuwa suka amsa, suka ce, A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.

"Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

"An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, Ranka daɗe! Ranka daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!

"Amma ya amsa ya ce, Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.

"Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

Jesus enfatiza a necessidade de estarmos sempre preparados espiritualmente para Sua segunda vinda, pois ninguém sabe o momento exato.

As parábolas de Jesus continuam sendo fontes ricas de sabedoria e direção para a vida cristã. Ao aplicarmos esses ensinamentos, nos aproximamos mais de Deus e de Sua vontade.

Se este artigo te ajudou, faça sua parte e compartilhe a Palavra de Deus com aqueles que você ama.

Seja o primeiro