Publicidade

Páscoa

Por Bíblia Online

A Páscoa é a celebração suprema da redenção. Do cordeiro pascal no Egito ao Cordeiro de Deus que tira o pecado do mundo, ela aponta para o sacrifício e a vitória de Cristo.

A caminhada para a cruz

Jesus entrou em Jerusalém como Rei humilde, e a multidão o aclamou. Ele sabia do sofrimento que viria, mas caminhou em obediência até o fim.

Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,

"Hosanna ga Ɗan Dawuda!"

"Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!"

"Hosanna a cikin sama!"

Ya Ubangiji, ka cece mu;

Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.

Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji.

Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.

Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima!

Ki yi sowa, Diyar Urushalima!

Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki,

mai adalci yana kuma da ceto,

mai tawali’u yana kuma hawan jaki,

yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.

"Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!"

A paixão de Cristo

Jesus foi zombado, açoitado e crucificado. Ele orou no Getsêmani e entregou sua vida voluntariamente, dizendo: 'Está consumado!'

Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, "Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!"

Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce,

Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

Ya ce, "Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so."

Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, "Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka." Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.

Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, "An gama." Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.

A ressurreição gloriosa

Ele não está aqui — ressuscitou! O túmulo vazio é a prova de que a morte foi derrotada e Cristo vive para sempre.

Mala’ikan ya ce wa matan, "Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta.

Ya ce, "Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.

Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ "

A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-22_10-02-25-