Publicidade

Paz

Por Bíblia Online

A paz é um dos frutos do Espírito e uma promessa central de Jesus: 'Deixo-vos a paz, a minha paz vos dou.' A Bíblia nos chama a buscar, cultivar e viver na paz de Deus.

A paz de Cristo

Jesus é o Príncipe da Paz. Antes de partir, prometeu aos discípulos uma paz que o mundo não pode dar nem tirar — paz sobrenatural em meio às tribulações.

Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."

"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."

Gama a gare mu an haifa mana yaro,

a gare mu an ba da ɗa,

gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.

Za a ce da shi

Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

Uban Madawwami, Sarkin Salama.

Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, "Salama a gare ku!"

Paz com Deus

Justificados pela fé, temos paz com Deus por meio de Cristo. Ele é a nossa paz, que derrubou a barreira e nos reconciliou.

Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,

Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.

ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka.

Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

A paz que excede o entendimento

A paz de Deus, que excede todo entendimento, guarda nosso coração e mente. Ela vem da confiança no Senhor e da entrega total a Ele.

Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Za ka kiyaye shi da cikakken salama

shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

domin ya dogara a gare ka.

Za ka kiyaye shi da cikakken salama

shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

domin ya dogara a gare ka.

Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

Promotores da paz

Bem-aventurados os pacificadores, porque serão chamados filhos de Deus. A Escritura nos chama a buscar e promover a paz em todos os relacionamentos.

Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,

gama za a kira su ’ya’yan Allah.

Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,

gama za a kira su ’ya’yan Allah.

Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.

Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.

Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,

Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.

Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.

Gama,

"Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

yă kuma ga kwanaki masu kyau

dole yă ƙame harshensa daga mugunta

leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

Juyo daga mugunta ku yi alheri;

nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

Juyo daga mugunta ku yi alheri;

nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

O fruto da paz

A sabedoria que vem do alto é pacífica. O fruto da justiça se semeia em paz por aqueles que cultivam a paz com mansidão.

Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,

Aikin adalci zai zama salama;

tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

Paz interior e descanso

Aquietai-vos e sabei que Eu sou Deus. A paz do Senhor acalma tempestades, silencia medos e sustenta a alma em todo tempo.

"Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

za a ɗaukaka ni cikin duniya."

Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,

gama kai kaɗai, ya Ubangiji,

kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;

Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar

su kuma zauna da cikakkiyar salama.

Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali;

akwai sa zuciya domin mutum mai salama.

Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama,

kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.

Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama,

kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.

Ni mutum ne mai salama;

amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, "Shiru! Ku natsu!" Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.

Sai ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki."

"Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna."

Anunciadores da paz

Como são formosos os pés dos que anunciam boas novas de paz! O evangelho é a mensagem de paz para todos os povos.

Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, "Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!"

Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu

a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi

waɗanda suke shelar salama,

waɗanda suke kawo labari mai daɗi,

waɗanda suke shelar ceto,

waɗanda suke ce wa Sihiyona,

"Allahnki yana mulki!"

"Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,

a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu."

"Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!"

"Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!"

Duba, can a bisa duwatsu,

ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi,

wanda yake shelar salama!

Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda,

ki kuma cika wa’adodinki.

Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba;

domin za a hallaka su ƙaƙaf.

shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.

O Deus da paz

Que o Deus da paz esteja com todos vocês. Ele nos santifica por completo e nos guarda irrepreensíveis para a vinda do Senhor.

Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.

Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.

Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,

Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.

" ‘ "Ubangiji yă albarkace ku,

yă kuma kiyaye ku;

Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku,

yă kuma yi muku alheri;

Ubangiji yă dube ku da idon rahama,

yă kuma ba ku salama." ’

Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

" ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.

Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,

da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.

Za ku fita da farin ciki

a kuma bi da ku da salama;

duwatsu da tuddai

za su ɓarke da waƙa a gabanku,

dukan itatuwan jeji kuma

za su tafa hannuwansu.

"Babu salama ga mugaye," in ji Allahna.

Paz, santidade e unidade

A paz exige esforço: guardar a unidade do Espírito, evitar contendas e buscar a santidade. Sem paz e santidade, ninguém verá o Senhor.

Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.

Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.

Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.

Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji,

yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.

Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,

ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,

amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙa’ida, har ma ga Isra’ila na Allah.

Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.

Paz e fé

O Deus da esperança nos encha de paz e alegria no crer. Quem mantém o pensamento firme no Senhor experimenta paz perfeita.

Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;

Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;

hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,

ba su kuma san hanyar salama ba."

"Babu tsoron Allah a idanunsu."

Yesu ya ce wa macen, "Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya."

"Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’

In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.

In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.

"Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.

A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,

da kuma cikin inuwar mutuwa,

don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama."

Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.

Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,

lokacin yaƙi da lokacin salama.

Ba su san hanyar salama ba;

babu adalci a hanyoyinsu.

Sun mai da su karkatattun hanyoyi;

babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.

Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.

Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai.

Sa’ad da wahala ta zo,

za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.

waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka." ’

"Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai.

Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.

Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-20_17-16-08-