Planejamento
O planejamento é sábio, mas deve sempre se submeter à vontade de Deus. A Bíblia ensina que devemos planejar com prudência, mas confiar que Deus dirige nossos passos.
Planejar com sabedoria
Contar nossos dias nos ensina a ter coração sábio. O planejamento prudente é elogiado na Escritura como expressão de bom senso.
Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,
don mu sami zuciyar hikima.
"In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.
Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara,
amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
Faɗi 8
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki;
ka kasance da hikimar dainawa.
Deus dirige os passos
O coração do homem planeja, mas a resposta certa vem do Senhor. Seus caminhos são mais altos que os nossos, e seus planos prevalecem.
’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,
amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,
amma manufar Ubangiji ce takan cika.
"Gama tunanina ba tunaninku ba ne,
yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,"
in ji Ubangiji.
"Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa
tunanina kuma dabam da naku.
Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,
shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.
Confiança no plano de Deus
Os planos do Senhor são de paz e esperança. Ele revela seus segredos aos seus servos e guia com fidelidade cada caminho confiado a Ele.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu
ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
Bari yă biya maka bukatan ranka
yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,
gama na sa zuciyata a gare ka.
Ka nuna mini hanyar da zan bi,
gama a gare ka na miƙa raina.
Lokaci domin kowane abu
Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.
Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.
Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye
ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta
amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.