Publicidade

Poder de decisão

Por Bíblia Online

Deus nos deu o poder de escolher. A Bíblia mostra que nossas decisões têm consequências eternas e nos chama a escolher sabiamente — a vida, a fé e o caminho de Deus.

A responsabilidade de escolher

Escolhei hoje a quem servireis. Cada decisão molda nosso destino, e Deus nos convida a escolher o caminho da vida e da obediência.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Yoshuwa kuwa ya ce musu, "Ku ne shaidun kanku cewa kun zaɓi ku bauta wa Ubangiji."

Suka amsa suka ce, "I, mu ne shaidun kanmu."

"Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.

Decisões e consequências

Deus retribuirá a cada um segundo as suas obras. As Escrituras nos alertam que a mornidão espiritual e a resistência ao Espírito têm consequências sérias.

Allah, "Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi." Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.

"Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!

Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.

Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. Gama,

"A cikin ɗan lokaci kaɗan,

mai zuwan nan zai zo

ba kuwa zai yi jinkiri ba.

Amma,

"Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.

In kuwa ya ja da baya,

ba zan ji daɗinsa ba."

Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.

Decisão e fé

Decida com fé, entregue seus planos ao Senhor e aja com determinação. Deus guia os passos de quem se achega a Ele de coração.

Akan jefa ƙuri’a a kan cinya,

amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.

Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,

amma manufar Ubangiji ce takan cika.

Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,

shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.

Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni,

ba zan sha kunya ba.

Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara,

na kuma sani ba zan sha kunya ba.

Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.

Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ya’yansu a bayansu.

Bitrus ya amsa, "Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.

Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Graziela Milhorance
1 pessoa deu Amém
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-