Pular para o conteúdo
Publicidade

Preservação das escrituras

Por Bíblia Online

A Palavra de Deus permanece para sempre. As Escrituras foram preservadas por Deus ao longo dos milênios para instrução, consolação e guia de todas as gerações.

A Palavra eterna

Céus e terra passarão, mas as palavras de Deus jamais passarão. Sua Palavra é eterna, infalível e imutável — a verdade que sustenta tudo.

Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za taɓa shuɗe ba.

Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.

Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,

amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada."

Gama,

"Dukan mutane kamar ciyawa suke,

darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;

ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

amma maganar Ubangiji tana nan har abada."

Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. Gama,

"Dukan mutane kamar ciyawa suke,

darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;

ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

amma maganar Ubangiji tana nan har abada."

Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

A inspiração divina

Toda Escritura é inspirada por Deus. Homens santos falaram da parte do Senhor, e a Palavra escrita é a expressão fiel da vontade divina.

Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

A Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.

Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.

A Palavra como guia e tesouro

A Palavra de Deus é lâmpada para os pés, espada do Espírito e tesouro para o coração. Guardá-la e meditá-la nos protege do pecado.

Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata

don kada in yi maka zunubi.

Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;

sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

Kowace rana tana yin jawabi;

kowane dare yana nuna sani.

Ba magana, ba kalmar da aka hurta,

ba wani amon da aka ji daga gare su.

Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,

kalmominsu zuwa iyakokin duniya.

A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,

kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yi tsere.

Takan taso daga ƙarshen sammai

ta kewaye zuwa wancan;

babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

Dokar Ubangiji cikakkiya ce,

takan wartsakar da rai.

Farillan Ubangiji abin dogara ne,

suna mai da hikima da sauƙi.

Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,

suna ba da farin ciki ga zuciya.

Umarnan Ubangiji haske ne

suna ba da haske ga idanu.

Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,

kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,

aka tsabtacce sau bakwai.

Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya

ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

Amma mene ne aka ce? "Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka," wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. Amma ina tambaya, "Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji.

"Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya,

kalmominsu kuma har iyakar duniya."

Gama duk abin da aka rubuta a an rubuta ne domin koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.

Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.

Seja o primeiro