Protecção e segurança
Deus é nosso protetor e refúgio seguro. Em todas as circunstâncias, a Bíblia nos assegura que o Senhor guarda, sustenta e protege aqueles que nele confiam.
Deus, a nossa fortaleza
O Senhor é refúgio e fortaleza, socorro bem presente na angústia. Quem habita no esconderijo do Altíssimo descansa à sombra do Todo-Poderoso.
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
Zan ce game da Ubangiji, "Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara."
Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
Ubangiji ne haskena da cetona,
wa zan ji tsoro?
Ubangiji ne mafakar raina,
wane ne zan ji tsoro?
Shi kaɗai ne dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
O escudo do Senhor
Deus nos rodeia com sua proteção como um escudo. Ele é rocha, baluarte e libertador. Sua fidelidade nos cobre e nos guarda.
Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!
Su nawa suke gāba da ni!
Da yawa suna magana a kaina suna cewa,
"Allah ba zai cece shi ba." Sela
Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,
ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela
Na kwanta na yi barci;
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
Ba zan ji tsoro ko dubu goma
suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;
maganar Ubangiji marar kuskure ne.
Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
Ka ba ni garkuwar nasara,
kuma hannunka na dama yana riƙe ni;
ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,
don kada ɗiɗɗigena yă juya.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena,
wanda ya horar da hannuwana don yaƙi,
yatsotsina don faɗa.
Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata,
katangata da mai cetona,
garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi,
wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.
ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara,
wanda ya cece bawansa Dawuda.
Daga takobin kisa.
Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai;
kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa.
Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini;
ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.
Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,
kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu
da hannunka na dama.
Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;
ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,
daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji
ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka
ba zai jijjigu ba.
Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka;
hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
A lokacin bayyanarka
za ka sa su zama kamar wutar matoya.
Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su,
kuma wutarsa za tă cinye su.
Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
Segurança e provisão
O Senhor supre todas as necessidades dos seus filhos. Quem busca o Reino primeiro não precisa temer — nada faltará aos que temem ao Senhor.
Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,
duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba
ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.
Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.
Roƙa, nema, ƙwanƙwasa
"Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
Guarda e livramento
O anjo do Senhor acampa ao redor dos que o temem e os livra. Deus promete guardar todas as nossas saídas e entradas para sempre.
Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
Ubangiji yakan cece bayinsa;
ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila
ba ya gyangyaɗi ko barci.
Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;
bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki
yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
Bari mutunci da adalci su tsare ni,
domin begena yana a kanka.
Dogara a kan doki don ceto banza ne;
duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
Confiança inabalável
Melhor é confiar no Senhor do que confiar no homem. Quem anda em integridade anda seguro, e a torre forte do nome do Senhor protege o justo.
Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka
zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
Mai mutunci yana tafiya lafiya,
amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
"Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;
shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
"Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;
shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
Adalci yakan lura da mutum mai mutunci,
amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
Masu adalci sukan ci isashen abinci,
amma cikin mugaye na fama da yunwa.
Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce,
marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
Akan shirya doki domin ranar yaƙi,
amma nasara tana ga Ubangiji ne.
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
A presença protetora
O Senhor prometeu estar conosco e nunca nos desampara. Ele é como sombra à nossa direita e fortaleza em todo o tempo.
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."
Allah madawwami shi ne mafakarka,
a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne.
Zai kore abokin gābanka a gabanka,
yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’
Game da Benyamin ya ce,
"Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi,
gama yana tsare shi dukan yini,
wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa."
ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,
za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.
Wannan ne gādon bayin Ubangiji,
kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,"
in ji Ubangiji.
Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura
ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.
Na yi ku zan kuma riƙe ku;
zan lura da ku
in kuma kuɓutar da ku.
Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama
haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;
zai kāre ta ya kuma fanshe ta,
zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita."
Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.
Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.
Ku ba wa marayu hakkinsu,
ku taimaki gwauruwa.
In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,
za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,
za a kashe ku da takobi."
Ni Ubangiji na faɗa.
Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum."
Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
Promessas de cuidado
Deus garante que nem um fio de cabelo cairá sem sua permissão. Ele deseja que vivamos em paz, confiança e segurança total nele.
Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a."
Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, "Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?"
Suka amsa, "Babu."
Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
"Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?"
Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.
Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
Fidelidade e aliança
Deus é fiel à sua aliança. Ele protege cada promessa que faz e guarda os seus como a menina dos seus olhos.
Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.
Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.
Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
In ya gamshe ka, bari ka albarkaci gidan bawanka don yă dawwama a gabanka har abada; gama kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka riga ka yi magana, kuma saboda kai ka sa albarka ga gidan bawanka, lalle zai kasance da albarka har abada."
Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.
Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.
" ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar.
Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba."
Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu
ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
Provisão diária
Deus satisfaz os desejos do coração dos seus filhos. Ele abençoa, renova as forças e sustenta dia após dia quem nele confia.
Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;
dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,
amma za a rufe bakunan maƙaryata.
Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu,
wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela
Ni ne Ubangiji Allahnku
wanda ya fitar da ku daga Masar.
Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;
Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;
ba ya hana kowane abu mai kyau
wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta,
gama yana tsaron rayukan amintattunsa
yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
Ubangiji yana tsare masu tawali’u;
sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.
Ka kwantar da hankali, ya raina,
gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.
Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa,
idanuna daga hawaye,
ƙafafuna daga tuntuɓe,
don in iya tafiya a gaban Ubangiji
a ƙasar masu rai.
Kai ne mafakata da garkuwata;
na sa zuciyata a maganarka.
In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,
masu gininta suna wahala a banza ne.
In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,
masu tsaro suna yin tsaro a banza.
"A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda
in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
Zan suturta abokan gābansa da kunya,
amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya."
Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.
Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
Yakan biya bukatun mutanen da aka danne
ya kuma ba da abinci ga mayunwata.
Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,
Ubangiji yakan ba wa makafi ido,
Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,
Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.
Ubangiji yana tsaron baƙi
yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa,
amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.
Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.
Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.
"Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi.
"Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’
"A wajen zakka da hadayu. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.
Hikima mafaka ce
takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.
Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita
ita ce amfanin ilimi.
Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.
Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi."
Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.