Proximidade
Deus é próximo dos que o buscam. Ele não é um Deus distante, mas presente, íntimo e acessível a todo o que o invoca com sinceridade de coração.
Buscar a presença de Deus
A Bíblia nos exorta a buscar a face do Senhor continuamente. Quem se aproxima dele encontra plenitude de alegria e delícias perpétuas.
Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Rana guda a filayen gidan sun fi
dubu a wani wuri dabam;
zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna
da in zauna a tentunan mugaye.
Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
Deus está perto
O Senhor está perto dos que o invocam, dos quebrantados de coração e dos que clamam por socorro. Sua presença nos sustenta.
Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.
Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
A presença que nunca abandona
Deus promete nunca nos deixar. Ele permanece fiel, está conosco em todo tempo e envia o Espírito para habitar em nossos corações.
Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu.
Amma cikin tausayinka mai girma ba ka kawo su ga ƙarshe ko ka yashe su ba, gama kai Allah ne mai alheri da kuma mai jinƙai.
Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa.
Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.
Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’
Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded. Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, "Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku. Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka. Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi. A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa. Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku."
Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.
Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa. A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita. Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu. Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni. Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.
Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe.
Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa.