Publicidade

Sabedoria

Por Bíblia Online

A sabedoria é um dos temas mais ricos da Bíblia. O temor do Senhor é seu princípio, e buscá-la vale mais que ouro ou prata. Deus promete dar sabedoria generosamente a quem pedir com fé.

O princípio da sabedoria

O temor do Senhor é o início de toda sabedoria verdadeira. Quem reverencia a Deus aprende a viver com discernimento e prudência.

Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

amma wawaye sun rena hikima da horo.

"Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,

kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;

dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.

Gare shi ne madawwamin yabo.

Amma a ina ne za a iya samun hikima?

Ina fahimta take zama?

Mutum bai gane muhimmancinta ba,

ba a samunta a ƙasar masu rai.

Zurfi ya ce, "Ba ta wurina";

teku ya ce, "Ba ta wurina."

Ba irin zinariyar da za iya sayenta,

ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,

ko sauran duwatsu masu daraja ba.

Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,

ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya;

farashin hikima ya fi na lu’uluai.

Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba,

zallar zinariya ma ba isa ta saye ta ba.

"To, daga ina ke nan hikima ta fito?

Ina fahimta take zama?

An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai,

har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.

Hallaka da mutuwa suna cewa,

Jita-jitarta kaɗai muke ji.

Sabedoria como dom de Deus

A verdadeira sabedoria vem do alto. Deus a concede generosamente a quem pede com fé, sem lançar em rosto a fraqueza humana.

In waninku ya rasa hikima, ya kamata roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

In waninku ya rasa hikima, ya kamata roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

In waninku ya rasa hikima, ya kamata roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

Gama Ubangiji yana ba da hikima,

daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.

Gama Ubangiji yana ba da hikima,

daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.

in kuma ka kira ga tsinkaya

ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,

to, za ka gane tsoron Ubangiji

ka kuma sami sanin Allah.

Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.

Kai ka san hikima da iko,

ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki."

Ya ce,

"Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;

hikima da iko nasa ne.

Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

A sabedoria do alto

A sabedoria que vem de Deus é pura, pacífica, amável, cheia de misericórdia e de bons frutos. Ela se opõe à sabedoria terrena e mundana.

Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

Hikima iri biyu

Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.

Hikima daga Ruhu

Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun , take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.

amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa "wawa" don zama mai hikima.

Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa "wawa" don zama mai hikima.

Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.

Direção e discernimento

Deus guia os humildes na justiça e ensina seu caminho aos mansos. Ele promete dirigir nossos passos quando confiamos nele de todo o coração.

Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

kada kuma ka dangana ga ganewarka;

cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

Kada ka zama mai hikima a ganinka;

ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;

Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.

Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai

ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,

ka koya mini hanyoyinka;

ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

gama kai ne Allah Mai cetona,

kuma begena yana a kanka dukan yini.

In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,

zai sa sawu su kahu;

Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

gama na sa zuciyata a gare ka.

Ka nuna mini hanyar da zan bi,

gama a gare ka na miƙa raina.

Ka koya mini in yi nufinka,

gama kai ne Allahna;

bari nagarin Ruhunka

bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;

a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.

Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;

ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya

saboda masu danne ni.

A Palavra como fonte de sabedoria

A Palavra de Deus é lâmpada para os pés e luz para o caminho. Meditar nas Escrituras nos dá entendimento superior ao dos mestres.

Maganarka fitila ce ga ƙafafuna

haske kuma a kan hanyata.

Maganarka fitila ce ga ƙafafuna

haske kuma a kan hanyata.

Ka buɗe idanuna don in iya gani

abubuwan banmamaki a cikin dokarka.

Fassarar maganganunka sukan ba da haske;

sukan ba da ganewa ga marar ilimi.

Mai farin ciki ne mutumin

da ba ya aiki da shawarar mugaye

ko yi abin da masu zunubi suke yi

ko zauna tare da masu yin ba’a.

Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,

kuma yana ta nazarinta dare da rana.

Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;

sa’ad da kake barci, za su lura da kai;

sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.

Sabedoria prática para o dia a dia

A sabedoria se aplica em cada decisão: nas finanças, nos relacionamentos, no trabalho e no uso do tempo. Vivamos como sábios, não como insensatos.

Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.

Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.

Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni,

a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.

Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni,

a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.

Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa;

duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.

Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara;

in kana yaƙi, ka sami bishewa.

don yin yaƙi kana bukatar bishewa,

kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.

Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa,

amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,

amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa,

amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.

Hanyar wawa daidai take a gare shi,

amma mai hikima kan saurari shawara.

Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,

amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.

Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni

amma surutun wawa kan kai ga lalaci.

Zuciya mai la’akari kan nemi sani;

kunnuwan mai hikima kan bincika don koya.

Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta

amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

bari masu tunani kuma su sami jagora,

Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.

O valor da sabedoria

A sabedoria é mais preciosa que rubis. Quem a encontra, encontra a vida e alcança o favor do Senhor. Nada se compara a ela.

Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,

mutumin da ya sami fahimi,

Gama duk wanda ya same ni ya sami rai

zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,

ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!

Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,

amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.

Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,

amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.

Hikima mafaka ce

takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.

Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita

ita ce amfanin ilimi.

Kada ka ce, "Me ya sa kwanakin sun fi waɗannan?"

Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.

Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

A sabedoria e a soberania de Deus

Os caminhos de Deus são mais altos que os nossos. Sua sabedoria é insondável, eterna e infinitamente superior ao entendimento humano.

"Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

tunanina kuma dabam da naku.

"Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,"

in ji Ubangiji.

Ba ku sani ba?

Ba ku ji ba?

Ubangiji madawwamin Allah ne,

Mahaliccin iyakokin duniya.

Ba zai taɓa gaji ko kasala ba,

kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

Ba ku sani ba?

Ba ku ji ba?

Ubangiji madawwamin Allah ne,

Mahaliccin iyakokin duniya.

Ba zai taɓa gaji ko kasala ba,

kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,

don in san maganar da za ƙarfafa gajiyayye.

Ya farkar da ni da safe,

ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.

Kaiton waɗanda suke dogara ga Masar

Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,

waɗanda suke dogara ga dawakai,

waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu

da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,

amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,

ko ya nemi taimako daga Ubangiji.

Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;

ba ya janye kalmominsa.

Zai yi gāba da gidan mugu,

gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.

Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,

shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.

Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,

Ruhun hikima da na fahimta,

Ruhun shawara da na iko,

Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,

zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.

Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,

ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;

Ubangiji zai bishe ku kullum;

zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana

ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku.

Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa,

kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.

Ɗaukakawa

Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin.

Fiye da masu nasara

Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!

Cikin hikima ka yi su duka;

duniya ta cika da halittunka.

Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

ganewarsa ba shi da iyaka.

Ka bishe ni da shawararka,

bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,

don mu sami zuciyar hikima.

Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima,

harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.

Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka

saboda abokan gābana,

ka fayyace hanyarka a gabana.

Ka sanar da ni hanyar rai;

za ka cika ni da farin ciki a gabanka,

da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

Za su zo da kuka;

za su yi addu’a yayinda nake komo da su.

Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa

a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba,

domin ni ne mahaifin Isra’ila,

Efraim kuma ɗan farina ne.

Addu’ar Irmiya

Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne;

ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba.

Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;

ya kafa duniya ta wurin hikimarsa

ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.

Kada ka yi fariya a kan gobe

gama ba san abin da ranar za kawo ba.

Mugaye ba su san gaskiya ba,

amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.

Gargaɗin ƙarshe

Wannan za zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. "Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku."

Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ya’ya,

"Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,

kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa."

A ƙarshe, yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

Sarauniyar Sheba za tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.

Magini mai hikima da marar hikima

"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.

Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci."

Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya,

ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;

Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?

Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?

"Allah ne mai iko da kuma hikima,

shawara da ganewa nasa ne.

Ayuba

Sai Ayuba ya amsa,

"Lalle, na san wannan gaskiya ne.

Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

Ko da mutum yana so yi gardama da shi,

ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.

Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa.

Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

Ya faɗa musu, "Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.

Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan ɓace.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-