Salvação
A salvação é a obra suprema de Deus. Pela graça, mediante a fé, somos salvos — não por obras, para que ninguém se glorie. É o presente mais precioso que a humanidade pode receber.
A salvação pela graça
A salvação é dom de Deus, não resultado de esforço humano. Somos justificados pela fé em Cristo Jesus e reconciliados com Deus pelo seu amor.
Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.
sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,
wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal,
Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai.
gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,
Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
O caminho da salvação
Quem confessa Jesus como Senhor e crê em sua ressurreição será salvo. A fé em Cristo é o único caminho para a salvação.
Cewa in ka furta da bakinka, "Yesu Ubangiji ne," ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
Suka amsa suka ce, "Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka."
Suka amsa suka ce, "Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka."
Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto."
Kuma duk wanda ya kira
bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
Yesu ya amsa ya ce, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah
Nova vida em Cristo
Quem está em Cristo é nova criação. A salvação não é apenas perdão, mas transformação completa — de dentro para fora, para a glória de Deus.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa."
Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.
Segurança eterna
O crente tem a certeza da salvação. Ninguém pode arrebatar da mão de Deus aqueles que Ele chamou, justificou e glorificou.
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa."
Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.
A salvação presente e futura
A salvação é passada (justificação), presente (santificação) e futura (glorificação). Deus nos salva, nos guarda e nos conduz à vida eterna.
Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,
Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!
Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.
Nada é impossível para Deus
Aos homens é impossível, mas para Deus tudo é possível. Ele deseja que todos sejam salvos e cheguem ao conhecimento da verdade.
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah."
Yesu ya amsa ya ce, "Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah."
Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma."
Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,
" ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai,
don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’"
"Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.
Yesu ya ce, "Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;
cetona na zuwa daga gare shi.
Ka ba ni garkuwar nasara,
kuma hannunka na dama yana riƙe ni;
ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,
don kada ɗiɗɗigena yă juya.
Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,
ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi,
ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,
gonaki kuma ba su ba da abinci ba,
ko da yake babu tumaki a garke,
ba kuma shanu a turaku,
duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,
zan yi murna da Allah Mai Cetona.
Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,
saboda kuma ina ƙaunarku,
zan ba da mutane a maimakonku,
al’umma kuma domin ranku.