Publicidade

Santidade

Por Bíblia Online

A santidade é o chamado supremo de Deus para o seu povo. 'Sede santos, porque eu sou santo' — essa ordem ressoa por toda a Escritura, convidando-nos a uma vida separada para Deus.

O chamado à santidade

Deus nos escolheu antes da fundação do mundo para sermos santos. A santificação é sua vontade expressa e nosso destino em Cristo.

Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; gama a rubuce yake cewa, "Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne."

Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; gama a rubuce yake cewa, "Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne."

Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.

Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; cikin wannan al’amari kuwa kada wani yi wa ɗan’uwansa laifi ko cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.

wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal,

O Deus santo

O Senhor é santo em toda a sua natureza. O universo testemunha sua santidade, e os anjos proclamam: Santo, Santo, Santo.

Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;

kai ne yabon Isra’ila.

"Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji

babu wani, in ban da kai;

babu wani dutse kamar Allahnmu.

Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa

wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne,

"Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri,

amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu,

don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u

in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.

Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.

Zan nuna tsarkin girman sunana, wanda aka ɓata a cikin al’umma, sunana da kuka ɓata a cikinsu. Sa’an nan al’ummai za su san cewa ni ne Ubangiji, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinku a idanunsu.

A prática da santidade

A santidade se expressa em pensamentos puros, ações corretas e separação do pecado. É um processo contínuo de purificação e dedicação a Deus.

Gargaɗi game da ƙin Allah

Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.

Gargaɗi game da ƙin Allah

Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.

Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.

Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.

Amma a yanzu da aka yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.

Hadayu masu rai

Saboda haka, ina roƙonku, yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

Ina roƙonku, yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.

Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.

Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.

sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta , wadda take lalacewa saboda sha’awace-shaawacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

A kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.

A Palavra que santifica

Jesus disse: 'Santifica-os na verdade; a tua palavra é a verdade.' A Bíblia é o instrumento de Deus para nos purificar e transformar.

Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.

Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?

Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.

Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata;

ka gwada ni ka kuma san damuwata.

Duba ko akwai wani laifi a cikina,

ka bishe ni a madawwamiyar hanya.

Yabi Ubangiji, ya raina;

dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

Templo do Espírito Santo

Nosso corpo é templo de Deus. Devemos honrá-lo com santidade, guardando mente e coração e buscando a semelhança com Cristo.

Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?

Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.

A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

Koyi tawali’un Kiristi

In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, to, sai ku sa farin cikina zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai kula da sha’anin waɗansu ma.

A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,

bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

amma ya mai da kansa ba kome ba,

yana ɗaukan ainihin surar bawa,

aka yi shi cikin siffar mutum.

Aka kuma same shi a kamannin mutum,

ya ƙasƙantar da kansa

ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,

mutuwar ma ta gicciye!

Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

don a sunan Yesu kowace gwiwa za durƙusa,

a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

kowane harshe kuma furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

don ɗaukakar Allah Uba.

Haskaka kamar taurari

Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, don ku zama marasa abin zargi, sahihai ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.

Timoti da Afaforiditus

Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan. Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.

Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin biya mini bukatuna. Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, domin ya kusa mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

Fitila a kan wurin ajiye fitila

"Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.

Ku yi nagarta, ba mugunta ba;

don ku rayu

sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,

kamar yadda kuka ce zai yi.

"Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani

daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.

Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.

Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.

" Ku tsarkake kanku, ku kuma zama da tsarki, gama Ni ne Ubangiji Allahnku.

Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,

ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;

sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.

Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-