Pular para o conteúdo
Publicidade

Sexo

Por Bíblia Online

A Bíblia trata a sexualidade como um presente de Deus para o contexto do casamento. As Escrituras celebram a intimidade conjugal e orientam sobre pureza e santidade sexual.

A sexualidade no plano de Deus

Desde a criação, Deus projetou a intimidade sexual como expressão de amor entre marido e mulher, abençoando a união conjugal.

Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

Miji da mace ya halicce su.

Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Ya amsa ya ce, "Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ya yi su namiji da ta mace, ya kuma ce, Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda? Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum raba."

Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

bari mamanta su ishe ka kullum,

bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

A santidade na intimidade

O leito conjugal é honroso. A Bíblia celebra a alegria da intimidade dentro do casamento e orienta o casal ao amor e respeito mútuo.

Aure zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

Ya kamata miji cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.

Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, "Biyun za su zama jiki ɗaya." Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

Pureza sexual

Deus nos chama à santificação e à fuga da imoralidade. O corpo do cristão é templo do Espírito Santo e deve ser tratado com honra.

Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;

Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.

Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.

Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.

Ba za ka yi zina ba.

" Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yi jima’i. Ni ne Ubangiji.

" Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.

" Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.

" Kada ka yi jima’i da yar’uwarka, ko yar mahaifinka ko yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.

" Kada ka yi jima’i da yar ɗanka ko yar yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.

" Kada ka yi jima’i da yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita yar’uwarka ce.

" Kada ka yi jima’i da yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.

" Kada ka yi jima’i da yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.

" Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.

" Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.

" Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.

" Kada ka yi jima’i da mace da kuma yarta. Kada ka yi jima’i da yar ɗanta ko yar yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.

" Kada ka auri yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.

" Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.

" Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.

" Kada ku ba da wani daga cikin ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.

" Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.

" Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za ba da kanta ga dabba don yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.

Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-shaawacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-shaawacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

Seja o primeiro