Temor do Senhor
O temor do Senhor é o princípio da sabedoria. Não se trata de medo, mas de reverência profunda, respeito e admiração diante da santidade e grandeza de Deus.
O princípio da sabedoria
A Escritura afirma que temer ao Senhor é o primeiro passo para a verdadeira sabedoria. Quem teme a Deus discerne o certo e aprende a viver com prudência.
Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
"Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
Ya kuma ce wa mutum,
‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,
kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ "
Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,
zai kasance har abada.
Farillan Ubangiji tabbatattu ne,
kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
Sun fi zinariya daraja,
fiye da zalla zinariya nesa;
sun fi zuma zaƙi
fiye da zuma daga kaki.
Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;
a kiyaye su akwai lada mai girma.
Bênçãos do temor
Quem teme ao Senhor encontra vida longa, provisão e proteção. O temor de Deus nos guarda do mal e nos conduz à humildade.
Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai,
amma akan gajartar da shekarun mugaye.
Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi;
ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah,
amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.
Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
Vivendo no temor do Senhor
Temer ao Senhor é obedecer seus mandamentos, andar em seus caminhos e amá-lo de todo coração. Essa reverência se expressa em justiça e integridade.
Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.
Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.
Ku bauta wa Ubangiji da tsoro
ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
zan koya muku tsoron Ubangiji.
Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci."
" ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.
" ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.
"Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.