Vida
A vida é um dom precioso de Deus. Desde a concepção até a eternidade, as Escrituras revelam o propósito, o valor e a plenitude da vida que o Senhor nos oferece.
Deus, o autor da vida
O Senhor é quem dá a vida e a sustenta. Cada ser humano foi formado por suas mãos com propósito e intenção divina.
Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai
cikin haskenka mukan ga haske.
Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
A vida em Cristo
Jesus é o caminho, a verdade e a vida. Nele encontramos sentido, plenitude e a promessa de vida abundante e eterna.
Yesu ya amsa ya ce, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?"
Sa’an nan Yesu ya furta cewa, "Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa."
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
Vivendo com sabedoria
A Bíblia nos orienta a viver com sabedoria, aproveitando bem o tempo, guardando o coração e buscando a vontade de Deus para cada dia.
Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,
don mu sami zuciyar hikima.
Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa,
shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa;
duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa,
amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai,
amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.
Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna
kan sami rai, wadata da girmamawa.
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
A vida no dia a dia
Cada dia é uma oportunidade de glorificar a Deus. A Escritura nos chama a viver com propósito, confiança e fé prática.
Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,
ka koya mini hanyoyinka;
Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
Jikina da zuciyata za su iya raunana,
amma Allah ne ƙarfin zuciyata
da kuma rabona har abada.
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata,
saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Ka natsu a gaban Ubangiji
ka kuma jira da haƙuri gare shi;
kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,
sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
Ba zan taɓa manta da farillanka ba,
gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
Prioridades e eternidade
Jesus nos lembra que a vida é mais que comida e o corpo mais que roupa. O que importa é buscar o Reino de Deus e viver para a eternidade.
"Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?
Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?
Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, "Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni. Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku."
Sai ya ce musu, "Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba."
Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba.
Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.
Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
Gama,
"Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,
yă kuma ga kwanaki masu kyau
dole yă ƙame harshensa daga mugunta
leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;
dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji.
Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne,
ko tamanin, in muna da ƙarfi;
duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai,
gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
"Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata
da kuma yawan kwanakina;
bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai;
yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka.
Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum,
har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela
"Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa.
Yana ta yawo, amma a banza ne kawai;
yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.
Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
Furfura rawani ne mai daraja;
akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take,
haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.