Hikima daga Ruhu
6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.