Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Coríntios 7

Aure

1 To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum zauna ba aure.7.1 Ko kuwa "Ya fi kyau kada mutum yă yi jima’i da mace." 2 Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3 Ya kamata miji cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4 Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5 Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

Veja também