2 Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; 3 ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.