Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Sarakuna 18

41 Sai Iliya ya ce wa Ahab, "Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa." 42 Sai Ahab ya ruga don ci, sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa.

43 Ya ce wa bawansa, "Tafi ka dubi wajen teku." Sai bawan ya haura ya duba.

Ya ce, "Ba kome a can."

Sau bakwai Iliya ya ce, "Koma."

44 Sau na bakwai, bawan ya ce, "Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku."

Sai Iliya ya ce, "Je ka faɗa wa Ahab, Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama tare ka.’ "

45 Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também