15 Sai Ubangiji ya ce masa, "Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram. 16 Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi.