Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Sarakuna 2

Dawuda ya gargaɗe Solomon

1 Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, 2 "Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, 3 ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. 4 Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.

Veja também