19 Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa.
20 Ta ce, "Ina da ɗan roƙon da zan nema ka yi mini. Ina fata ba za ka hana ni ba."
Sai sarki ya amsa ya ce, "Mahaifiyata, sai ki faɗa in ji, ba zan hana miki ba."