Addu’ar Hannatu
1 Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce,
"Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji;
a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai.
Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya.
Kai! Ina murna domin ka cece ni!
2 "Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji
babu wani, in ban da kai;
babu wani dutse kamar Allahnmu.
3 "Ka daina maganganu na girman kai
ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai;
gama Ubangiji Allah ne masani
daga gare shi kuma ana auna ayyuka.
4 "An kakkarya bakkuna masu yaƙi,
amma su da ka raunana an ba su makaman ƙarfi.
5 Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci,
masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.
Ita da take bakararriya, ta haifi ’ya’ya bakwai
amma ita da tana da ’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki.
6 "Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar
yana kai ga kabari, yă kuma tā da.
7 Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya;
yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.
8 Yakan tā da matalauci daga ƙura,
yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka;
yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki;
yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka.
"Harsashin duniya na Ubangiji ne;
a bisansu ne ya kafa duniya.
9 Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki,
amma mugaye za su lalace cikin duhu.
"Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;
10 waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka.
Zai yi musu tsawa daga sama,
Ubangiji zai hukunta dukan duniya.
"Zai ba wa sarkinsa ƙarfi,
yă kuma ɗaukaka shafaffensa."