Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Timóteo 3

Masu kula da ikkilisiya da masu hidimar ikkilisiya

1 Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya,3.1 A al’adance bishob; haka ma a aya 2 yana marmarin yin aiki mai daraja ne. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4 Dole iya tafiyar da iyalinsa da kyau, kuma tabbata cewa ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5 (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?) 6 Kada zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. 7 Dole kuma kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada zama abin kunya kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

Veja também