3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.
Publicidade