Gafara don mai zunubi
5 In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne. 6 Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. 7 Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa. 8 Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.