Pular para o conteúdo
Publicidade

2 Bitrus 3

3 Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-shaawacensu. 4 Za su ce, "Ina wannan dawowarda ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta." 5 Amma da gangan suke manta cewa tun can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. 6 Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. 7 Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

2 Pedro
Ver todos os capítulos de 2 Pedro