Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila
1 Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, "Mu nama da jininka ne. 2 A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ "
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.