Rashin sanin Allah a kwanakin ƙarshe
1 Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. 2 Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, 3 marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,