13 Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. 14 Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.
Publicidade