Pular para o conteúdo
Publicidade

Atos 2

Bitrus ya yi wa taron jawabi

14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, "Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! 16 A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

17 "Allah ya ce, A kwanakin ƙarshe,

zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.

Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

samarinku za su ga wahayoyi,

dattawanku kuma za su yi mafarkai.

18 Kai, har ma a kan bayina, maza da mata,

zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki,

za su kuwa yi annabci.

19 Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama

da alamu a nan ƙasa,

jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.

20 Za a mai da rana duhu,

wata kuma ya zama jini,

kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.

21 Kuma duk wanda ya kira

bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.2.21 Yow 2.28-32

22 "Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. 23 An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. 24 Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25 Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa,

" Kullum ina ganin Ubangiji a gabana.

Gama yana a hannuna na dama,

ba zan jijjigu ba.

26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,

jikina kuma zai kasance da bege,

27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,

ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ruɓa ba.

28 Ka sanar da ni hanyoyin rai,

za ka cika ni da farin ciki a gabanka.2.28 Zab 16.8-11

29 "Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har zuwa yau. 30 Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa. 31 Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. 32 Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan. 33 An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji. 34 Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce,

" Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

"Zauna a hannun damana,

35 sai na sa abokan gābanka

su zama matashin sawunka." 2.35 Zab 110.1

36 "Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi."

37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, "Yan’uwa, me za mu yi?"

38 Bitrus ya amsa, "Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira."

40 Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, "Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani." 41 Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.

Veja também