42 Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa,
" ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?
43 Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek,
da tauraron allahnku Refan,
gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.
Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’7.43 Amos 5.25 gaba da Babilon.