Pular para o conteúdo
Publicidade

Ayyukan Manzanni 8

32 Bābān yana karanta wannan Nassin,

"An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka,

kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru,

haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.

33 A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya.

Wa zai iya yin zancen zuriyarsa?

Gama an ɗauke ransa daga duniya."8.33 Ish 53.7,8

34 Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, "Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?" 35 Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.

Veja também