21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23 Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
Publicidade