15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
Publicidade