Horarwar Daniyel a Babilon
1 A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya. 2 Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon1.2 Shinar na Ibraniyanci cikin ma’ajin gidan allahnsa.
3 Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane. 4 Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.1.4 Ko kuwa Kaldiyawa 5 Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.
6 Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya.