24 "An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.
25 "Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka9.25 Ko kuwa kalma don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan,9.25 Ko kuwa shafaffen nan; haka kuma a aya 26 mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka. 26 Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome.9.26 Ko kuwa ba zai kasance da kome ba; Ko kuwa a kawar, amma ba don kansa ba Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara. 27 Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai.9.27 Ko kuwa "mako" A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya9.27 Ko kuwa "mako" zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama."9.27 Ko kuwa shi (abin da ba mutum ba)9.27 Ko kuwa abin da zai kawo hallaka zai zo ne a kan ƙwanƙolin za tă zubo allahn birnin