5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
Publicidade