Lokaci domin kowane abu
1 Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,
lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,
lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 Lokacin kuka da lokacin dariya,
lokacin makoki da lokacin rawa.
5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,
lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,
lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,
lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,
lokacin yaƙi da lokacin salama.