Pular para o conteúdo
Publicidade

Êxodo 20

3 "Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

4 Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. 5 Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, 6 amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

7 Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11 Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

13 Ba za ka yi kisankai ba.

14 Ba za ka yi zina ba.

15 Ba za ka yi sata ba.

16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

17 Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba."

Veja também