10 To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar."
11 Amma Musa ya ce wa Allah, "Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?"
12 Sai Allah ya ce, "Zan kasance da tare kai. Wannan kuwa za tă zama alama a gare ka cewa Ni na aike ka. Bayan ka fitar da mutanen daga Masar, za ku yi sujada ga Allah a kan dutsen nan."