Pular para o conteúdo
Publicidade

Êxodo 32

11 Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, "Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma? 12 Don me za ka sa Masarawa su ce, Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don shafe su daga fuskar duniya? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka. 13 Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za kuma zama abin gādonsu har abada.’ " 14 Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.

Veja também