2 "Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,
" ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami,
haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?
3 "Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. 4 Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
20 Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.