Publicidade

Ezequiel 19

Makoki domin sarakunan Isra’ila

1 "Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila 2 ka ce,

" ‘Mahaifiyarki zakanya ce

cikin zakoki!

Takan kwanta cikin ’yan zakoki

ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.

3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,

ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi.

Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta

yakan kuma cinye mutane.

4 Al’ummai suka ji labarinsa,

aka kuma kama shi cikin raminsu.

Suka ja shi da ƙugiyoyi

zuwa ƙasar Masar.

5 " ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba,

abin da take fata gani ya tafi,

sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta

ta mai da shi zaki mai ƙarfi.

6 Ya yi ta yawo a cikin zakoki,

gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi.

Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta

yakan kuma cinye mutane.

7 Ya rurrushe kagaransu

ya kuma ragargaza biranensu.

Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta

sun tsorata da jin rurinsa.

8 Sai al’ummai suka tayar masa,

waɗannan daga yankunan da suke kewaye.

Suka yafa raga dominsa

ya kuwa fāɗa cikin raminsu.

9 Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji

suka kawo shi wurin sarkin Babilon.

Suka sa shi cikin kurkuku,

saboda haka ba a ƙara jin rurinsa

a kan duwatsun Isra’ila ba.

10 " ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi

da aka shuka kusa da ruwa;

ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa

saboda yalwan ruwa.

11 Rassanta suka yi ƙarfi,

suka dace da sandar mai mulki.

Ta yi tsayi

zuwa sama

ana ganin ta saboda tsayinta

da kuma saboda yawan rassanta.

12 Amma aka tumɓuke ta cikin fushi

aka jefar da ita a ƙasa.

Iskar gabas ta sa ta yanƙwane,

aka kakkaɓe ’ya’yanta;

rassanta masu ƙarfi suka bushe

wuta kuma ta cinye su.

13 Yanzu an shuka ta a hamada,

a busasshiyar ƙasa marar ruwa.

14 Wuta ta fito daga jikin rassanta

ta cinye ’ya’yanta.

Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta

da ya dace da sandar mai mulki.’

Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-