4 ya ce masa, "Ka ratsa birnin Urushalima ka sa shaida a goshin waɗanda suke baƙin ciki da kuma makoki a kan dukan abubuwan banƙyamar da ake yi a cikinsa."
5 Yayinda nake saurara, sai ya ce wa waɗansu, "Ku bi shi ta birnin ku kuma kashe, babu tausayi ko kuwa jinƙai. 6 Ku kashe tsofaffi da samari da ’yan mata, mata da yara, amma kada ku taɓa wani wanda yake da shaida. Ku fara a wuri mai tsarkina." Saboda haka suka fara da dattawan da suke gaban haikali.