Pular para o conteúdo
Publicidade

Filipenses 3

12 Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. 13 Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, 14 ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.

Nacewa zuwa ga manufar

15 Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.

Veja também

Filipenses
Ver todos os capítulos de Filipenses