3 Abram ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, Allah kuma ya ce masa, 4 "Gare ni kam, wannan shi ne alkawarina da kai, za ka zama mahaifin al’ummai masu yawa. 5 Ba za a ƙara kiranka Abram17.5 Abram yana nufin uban da aka ɗaukaka. ba; sunanka zai zama Ibrahim,17.5 Ibrahim yana nufin uban mutane da yawa. gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa. 6 Zan sa ka azurta sosai, zan yi al’ummai daga cikinka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka, 7 zan kafa alkawarina kamar madawwamin alkawari tsakanina da kai da kuma zuriyarka bayanka har tsararraki masu zuwa, in zama Allahnka da kuma Allahn zuriyarka a bayanka. 8 Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu."
9 Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. "Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. 10 Wannan shi ne alkawarina da kai da kuma zuriyarka a bayanka, alkawarin da za ka kiyaye ke nan. Kowane namiji a cikinku kuwa za a yi masa kaciya. 11 Za ku yi kaciya, za tă kuma zama alamar alkawari tsakanina da kai.