15 Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. 16 Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, "Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba." Da ta zauna nesa da yaron, sai ta21.16 Da Ibraniyanci; Seftuwajin yaron. fara kuka.