Pular para o conteúdo
Publicidade

Farawa 26

Ishaku da Abimelek

1 Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar. 2 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, "Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka. 3 Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim. 4 Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya, 5 domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina." 6 Sai Ishaku ya zauna a Gerar.

7 Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, "Yar’uwata ce," gama yana tsoro ce, "Ita matata ce." Ya yi tunani, "Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce."

8 Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka.

Veja também