Yusuf ya sanar da kansa
1 Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, "Kowa yă tashi daga gabana!" Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.
4 Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, "Ku zo kusa da ni." Da suka yi haka, sai ya ce, "Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar! 5 Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.
15 Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.