Pular para o conteúdo
Publicidade

Farawa 45

Yusuf ya sanar da kansa

1 Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, "Kowa tashi daga gabana!" Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga yan’uwansa. 2 Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.

3 Yusuf kuwa ya ce wa yan’uwansa, "Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?" Amma yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.

Veja também